Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : A zaman farko na juyayin shahadar Imam Hussain (AS) da aka fara gudanarwa a Husainiyar Imam Khomeini da ke birnin Tehran, Jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya halarci wurin kamar yadda ya saba yi a kowace sheakara.
Sai dai a shekarar bana kamar shekarar bara ne, inda aka takaita halartar jama’a a wurin, sakamakon matsaloli na kiwon lafiya da suka shafi yaduwar cutar corona.
Hujjatol Islam Siddiqi ne ya gabatar da jawabi, dangane da matsayin tafarkin da Imam Hussain (AS) da alayen manzon Allah suka yi shahada a kansa, inda ya bayyana cewa wannan yana a matsayin abin da yake fayyace hakikanin tafarkin manzon Allah (SAW) ne da kuma annabawan Allah amincin Allah ya tabbata a gare su.
342/